Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar an hukunta duk wadanda aka kama da hannu a sace dalibai da malamansu a jihar Oyo, tare da wadanda ke da hannu a kisan Mista Oyedokun.


Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake taya

jami'an tsaro murnar nasarar da suka samu wajen ceto daliban da malamansu bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.


A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan

harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yabawa sojoji, jami'an Hukumar Tsaro ta DSS da Rundunar 'Yan Sanda bisa gudanar da aikin ceton cikin nasara ba tare da rasa ran ko daya daga cikin wadanda aka sace ba.


Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun kashe akalla 'yan bindiga tara tare da kama mutum takwas a wani samame na hadin gwiwa da suka kai bisa bayanan sirri da Hukumar DSS ta tattara.


Shugaban kasar ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da yaki da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuffuka domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin

al'ummar Najeriya.