Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta gabatar da Daniel Ogunmodede a matsayin sabon mai horar da kungiyar, gabanin fara kakar wasannin Najeriya ta 2026/2027.
An gudanar da bikin gabatar da sabon kocin ne a ranar Asabar a sakatariyar kungiyar da ke Kano, inda Shugaban Kano Pillars, Alhaji Ahmed Musbahu Garo, tare da mambobin kwamitin gudanarwar kungiyar suka halarta.
Ogunmodede ya riga ya sanya hannu kan kwantiragin da zai jagoranci kungiyar, wadda ta taba lashe gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) har sau hudu.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan gabatar da shi, sabon kocin ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin mayar da Kano Pillars cikin manyan kungiyoyin kasar, yana mai cewa burinsa shi ne kungiyar ta fafata domin lashe manyan kofuna a kakar wasa mai zuwa.
Nadin Ogunmodede na zuwa ne yayin da Kano Pillars ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar sabon kakar wasa, tare da fatan dawo da martabarta a gasar NPFL bayan shekaru da dama na rashin samun babban nasara.