Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa an kuɓutar da dukkan ɗalibai da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Orire da ke jihar Oyo.
Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a.
A cewarsa, jami'an tsaro sun yi nasarar ceto duka waɗanda aka sace, tare da tabbatar da cewa sun koma cikin ƙoshin lafiya. Ya kuma wallafa hotuna da wani ɗan gajeren bidiyo da ke nuna ɗaya daga cikin malaman makarantar na bayyana farin cikinta bayan samun 'yanci.
Sai dai gwamnatin ba ta yi cikakken bayani kan yadda aka gudanar da aikin ceto ko kuma ko an kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen ba.
A ranar 15 ga Mayun 2026 ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wata makaranta a ƙaramar hukumar Orire, inda suka yi garkuwa da mutum 46, waɗanda suka haɗa da ɗalibai 39 da malamai bakwai.
A wani ɓangaren kuma, har yanzu ana ci gaba da jiran samun labarin ɗalibai sama da 40 da aka sace a wani makamancin hari da aka kai a jihar Borno.