Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake zaɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa domin neman wa'adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Jam'iyyar APC ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta bayyana cewa ta karɓi fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da aka cike.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya karɓi takardun a wani taro da aka gudanar a Abuja.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, ne ya miƙa takardun a madadin Shugaba Tinubu.

A cewar jam'iyyar, mataki na gaba shi ne miƙa takardun ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin ci gaba da sauran matakan da doka ta tanada na rajistar 'yan takara.

Matakin ya kawo ƙarshen rade-raɗin da aka daɗe ana yi cewa Shugaba Tinubu na iya sauya mataimakinsa kafin zaɓen 2027, musamman sakamakon muhawarar da aka yi kan tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta yi amfani da shi a zaɓen 2023.