Masar da Qatar sun yi kira ga Amurka da Iran da su dawo kan teburin tattaunawa domin neman mafita ta lumana ga rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Kiran ya fito ne daga Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdel Ati, da Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar, ministocin sun jaddada muhimmancin komawa kan hanyoyin diflomasiyya da sasanci, tare da buƙatar dukkan ɓangarorin su kauce wa matakan da za su ƙara tsananta rikicin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Ministan Harkokin Wajen Masar ya tattauna da takwarorinsa na Kuwait, Bahrain da Jordan domin haɗa kai wajen tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A nata ɓangaren, Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ta ce Sheikh Mohammed ya sake nanata muhimmancin ci gaba da tattaunawa da amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware saɓanin da ke tsakanin ƙasashe.
Wannan kira na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka na da niyyar ci gaba da tattaunawa da Tehran, duk da cewa ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin ta kawo ƙarshe.