Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce ta kashe gomman mayaƙan ƙungiyar Boko Haram a wani jerin hare-haren sama da ta kai kan wuraren ɓuyar ƙungiyar a Jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce an gudanar da samamen ne a yankin Yaganari da ke jihar Borno.
A cewarsa, hare-haren sun yi sanadin kashe gomman ‘yan ta’addan, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan da suka samu.
Ejodame ya ƙara da cewa hare-haren sun lalata sansanonin ‘yan ta’addan tare da tarwatsa cibiyoyin ayyukansu. Haka kuma, ya ce an ƙwace bama-bamai da aka haɗa da hannu (IEDs) da kuma makamai masu yawa a yayin samamen.
Ya bayyana cewa kafin ƙaddamar da hare-haren, rundunar ta gudanar da bincike ta sama wanda ya tabbatar da kasancewar kayayyakin ‘yan ta’addan da kuma cibiyoyin sufuri da suke amfani da su a yankin.
Rundunar ta ce hare-haren na daga cikin matakan da take ci gaba da ɗauka domin rage ƙarfin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da kuma tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.