Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin gabatar da sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya domin babban zaɓen shekarar 2027 da karin kwanaki uku.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta ce sabon wa’adin zai ƙare da ƙarfe 12:00 na dare ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, maimakon ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2026 da aka tsara tun farko.
Sanarwar, wadda shugaban kwamitin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na INEC, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafin da ƙungiyar Inter-Party Advisory Council (IPAC) ta gabatar a madadin wasu jam’iyyun siyasa da ba su samu damar kammala gabatar da sunayen da bayanan ‘yan takararsu cikin wa’adin da aka kayyade ba.
A cewar INEC, tsawaita wa’adin na nuni da aniyarta ta tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa sun samu damar shiga tsarin zaɓe cikin adalci tare da bin tanade-tanaden dokokin zaɓe.
Hukumar ta kuma buƙaci jam’iyyun siyasa da su yi amfani da wannan ƙarin lokaci wajen kammala loda dukkan bayanan ‘yan takararsu kafin sabon wa’adin ya cika.
“INEC na kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da cewa sun gabatar da cikakkun bayanai da ake buƙata kafin ƙarshen sabon wa’adin,” in ji sanarwar.