Amurka ta ƙaddamar da hare-haren soji kan wasu wurare a Iran bayan da dakarun Juyin Juya Halin Iran suka kai hari kan wani jirgin ruwan dakon kaya a ranar Asabar, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce matakin na Amurka ya biyo bayan harin da aka kai kan jirgin, yayin da Iran ke ci gaba da barazanar rufe Mashigin Ruwan Hormuz, wani muhimmin mashigi da ake jigilar kaso mai yawa na man fetur da iskar gas na duniya ta cikinsa.
Baya ga barazanar rufe mashigin, rahotannin sun kuma nuna cewa an kai hare-hare a wasu ƙasashen da ke yankin Tekun Fasha, abin da ya ƙara dagula yanayin tsaro da fargabar yiwuwar faɗaɗar rikicin.
Masu sa ido na ganin cewa ci gaba da takun-saƙar tsakanin Amurka da Iran na iya yin tasiri ga harkokin sufuri, kasuwancin makamashi da kuma zaman lafiyar yankin baki ɗaya.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan asarar rayuka ko irin barnar da hare-haren suka haifar ba.