Matasa da ɗalibai a Jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi domin nuna adawa da rashin tsaro, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa gwamnati baya su kuma haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da sauran nau’o’in laifuffuka a ƙasar.


Gangamin wayar da kan jama’a mai taken #UniteAgainstTerror ya haɗa ƙungiyoyin ɗalibai da na matasa daga sassa daban-daban na jihar. 


An gudanar da tattakin wayar da kan jama’ar ne a yankin Post Office da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.


Da yake zantawa da Jaridar PUNCH Online kai tsaye a wurin zanga-zangar, shugaban Matasa da Ɗalibai na Jihar Borno, Suleiman Muhammed, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa gaggawar da ta yi wajen ceto ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo, sannan ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da kuɓutar da dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su a Borno.


Muhammed ya kuma yi gargaɗi kan biyan kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda, yana mai cewa yin hakan zai ƙara ta’azzara matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.