Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) ta sanar da fara aikin kawo ƙarshen kwangilar kocin ƙungiyar ƙasa, Pape Thiaw, da ma'aikatansa, bayan ficewar Senegal daga gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026.

Matakin ya biyo bayan rashin nasarar da Senegal ta yi wajen kai wa zagaye na 16, bayan ta sha kashi a hannun Belgium da ci 3-2, duk da cewa ta fara wasan da cin ƙwallaye biyu babu ko ɗaya.

A cikin wata sanarwa, FSF ta bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne a wani taron kwamitin zartarwa da aka gudanar ranar Asabar, inda aka yi nazari kan yadda ƙungiyar ta taka leda da kuma sakamakon da ta samu a gasar.

Hukumar ta kuma ɗora wa shugabanta, Abdoulaye Fall, alhakin sanar da Pape Thiaw hukuncin a hukumance, tare da jagorantar wani sabon shiri na sake fasalin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙasar.

Ana sa ran Abdoulaye Fall zai yi wa manema labarai bayani a Dakar ranar Litinin, inda zai bayyana dalilan ɗaukar wannan mataki da kuma shirye-shiryen da hukumar ke yi na farfaɗo da ƙwallon ƙafar Senegal.

Kafin fara gasar ta 2026, masana da masu bibiyar ƙwallon ƙafa sun yi hasashen cewa Senegal za ta kasance cikin ƙasashen Afrika da za su iya taka rawar gani har ma su yi fafutukar lashe kofin duniya.