Mafarauta da hadin gwiwar rundunar JTF sun kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow.


An kashe shugaban ‘yan bindigar a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara bayan musayar wuta, inda suka jami'an tsaron suka dakushe wani hari da ‘yan bindigar sukayi yunkurin kai wa.


Kachalla Sani Yellow na daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindiga masu tasiri da suka addabi ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru a Jihar Zamfara.


An ce marigayi Kachalla Sani Yellow yana cikin kwamandojin ‘yan bindigar da suka jagoranci hare-haren haɗin gwiwa kan Mutanen da basu ji ba kuma ba su gani ba a sassan Arewa maso Yammacin kasarnan


Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kashe shi.


An yaɗa hotunan gawar shugaban ‘yan bindigar a shafukan sada zumunta.