Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sun sanar da samun nasara a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar, inda dakarun haɗin gwiwa suka yi nasarar cafke wasu ƴan bindiga 8 da suka kai hari.


Wannan kamen ya biyo bayan wani kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami'an tsaro, amma dakarun suka fatattake su.


Baya ga kama mutanen, jami'an tsaron sun yi nasarar kwace miyagun makamai masu tarin yawa, da sauran kayan yaki da ƴan ta'addan ke amfani da su wajen addabar al'ummar da ke makwabtaka da tafkin Chadi.


An gudanar da wannan aiki ne a yankin kan iyaka da Najeriya, biyo bayan harin da aka kai wa ofishin kwastan na Chéri da ke wannan sashe a daren 7 zuwa 8 ga watan Yuli.


Bayan kwashe sa'o'i 24 ana fafatawa, jami'an tsaro sun fatattaki maharan, kuma a yanzu haka suna hannun hukumomin sharia.