Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki rahotannin da ke cewa Gwamnatin tarayya ta amince da sanya kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi daga shekarar 2027.


A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce wannan mataki tare da ƙarin kuɗin makarantun Unity Colleges zai ƙara jefa iyaye cikin wahala tare da hana miliyoyin yara samun ilimi.


Ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa ƙara kuɗin jarabawa zai ƙara yawan yaran da za su rasa damar ci gaba da karatu, musamman daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.


Atiku ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya janye shirin ƙara kuɗin WAEC da NECO tare da rage kuɗin makarantun gwamnati, yana mai kira ga gwamnati ta ƙara zuba jari a fannin ilimi, faɗaɗa cibiyoyin ilimi da kuma tabbatar da cewa talauci bai hana kowane yaro samun ilimi ba.