Sojojin Najeriya sun hallaka fitaccen jagoran ’yan bindiga, Kacalla Sani Yellow, a yayin wani mummunan artabu da suka yi da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara.


Rahotanni sun ce an kashe Sani Yellow ne a lokacin wani samame da sojojin suka kai kan maboyar ’yan bindiga a yankin, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.


Baya ga Kacalla Sani Yellow, rahotannin sun nuna cewa sojojin sun kuma kashe wasu daga cikin mabiyansa a wannan farmaki. Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken adadin ’yan bindigar da aka kashe ba.


Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke ƙarin bayyana cikakken bayani kan farmakin ba.