Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya bayyana cewa hukumar na duba yiwuwar faɗaɗa gasar Kofin Duniya ta FIFA zuwa ƙasashe 64 masu halarta.
Infantino ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Blue News ta ƙasar Switzerland, inda ya ce kwamitocin da abin ya shafa a cikin FIFA za su yi nazari tare da tattauna wannan shawara nan gaba kaɗan.
A cewarsa, hukumar za ta bi dukkan matakan da suka dace kafin yanke hukunci kan yiwuwar ƙara yawan ƙasashen da za su halarci gasar.
Idan aka amince da wannan shiri, zai kasance wani babban sauyi a tarihin gasar Kofin Duniya, wadda tuni aka faɗaɗa ta daga ƙasashe 32 zuwa 48, wanda aka fara amfani da shi a gasar 2026 da ake gudanarwa a Amurka, Kanada da Mexico.
Sai dai kawo yanzu FIFA ba ta sanar da wata matsaya ta ƙarshe kan batun ba, yayin da ake sa ran kwamitocin hukumar za su ci gaba da nazarin shawarar kafin yanke hukunci.