Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin ƙara kuɗin jarabawar Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da ta Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Kasa (NECO), domin sake nazarin batun tare da tuntubar masu ruwa da tsaki.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bai wa gwamnati damar yin cikakken nazari kan shirin kafin yanke hukunci na ƙarshe.


Tun da farko, ma’aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin jarabawar daga N27,000 zuwa N50,000, wanda aka shirya zai fara aiki daga shekarar 2027.


A cewar ma’aikatar, dalilin ƙarin kuɗin ya samo asali ne daga hauhawar farashin kayayyaki da tsadar gudanar da jarabawa, tana mai cewa kuɗin da ake karɓa a halin yanzu ba ya iya biyan kuɗaɗen gudanar da jarabawar yadda ya kamata.


Sai dai sanarwar ta janyo ce-ce-ku-ce da suka daga sassa daban-daban na ƙasar, inda masu sukar shirin suka bayyana cewa ƙarin kuɗin zai ƙara wa iyaye da ɗalibai nauyi, tare da yiwuwar jefa wasu ɗalibai cikin barazanar daina karatu saboda rashin iya biyan kuɗin jarabawar.


Ma’aikatar ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki kafin ta fitar da sabon matsayi kan batun.