Shugaban hukumar Samar da magunguna ta Jihar Kano Pharm. Ghali Sule ne ya bayyana hakan ga manema Labarai, a yayin kaddamar da shirye shiryen da hukumar ta shirya don gudanar da bikin cikar Gwamna abba shakera uku da kokarin wadata Jihar kano da magunguna masu sauki a asibitoci.
Bikin da hukumar ta Fara a safiyar yau a harabarta dake nan Kano, da aka soma da saukar Alfur'qani mai girma, don Nasarar Gwamnan da wanzuwar zaman lafiya a kano.
Pharm. Ghali ya Kara da cewa, a ranar 14 za a gabatar da taron wayar da Kan mutane Kan aiyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Samar a Jihar Kano a fannin lafiya karkashin hukumar. Inda a ranar ta 16 hukumar zata Gudanar da Mukala ta musamman Kan wayar da Kai Kan illar sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Taron zai karbi bakoncin masana da malaman jiniya, likitocin kwakwalwa da kuma malamai, don fito da illar dake tattare da ta'ammali da miyagun kwayoyi.
Bikin zai kammala a Ranar 17 ga watan yuli, inda Gwamnan Kano Injiniya Abba kabir Yusuf zai kaddamar da babban rumbun ajiyar magani da babu irinsa.