Rundunar ’Yan Sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Talata bisa zargin kafa wata hukumar bogi da ya danganta da Fadar Shugaban Ƙasa.
Ana zargin Adeyemi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda hukumomi suka ce ba ta da wata halastacciyar amincewa daga gwamnati.
Shi da wasu mutum biyu na fuskantar tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da ƙirƙirar takardun bogi, yin sojan gona da sauran laifuka masu alaƙa da yaudara.
Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa Adeyemi ya kasance yana gudanar da ayyukan wannan hukuma ta bogi daga harabar Sakatariyar Tarayya da ke Abuja kafin jami’an tsaro su kama shi.
Takardun shari’ar sun nuna cewa masu gabatar da ƙara za su gabatar da shaidu da dama a gaban kotu, ciki har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu takardu da ake zargin an ƙirƙira su, ciki har da wasiƙun naɗin muƙami da wasiƙun da aka aika wa ma’aikatun gwamnati.
A wani ci gaba kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da cikakken bincike kan ayyukan wannan hukuma ta bogi, inda ya ba ta wa’adin kwanaki 30 domin kammala binciken.