Adadin ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai mataki mafi girma cikin fiye da shekara shida a watan Yuni, inda ya zarce kason da ƙungiyar OPEC ta ware wa ƙasar.


Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana cewa ƙididdigar da hukumomin da ke sa ido kan fannin haƙo mai suka fitar a ranar Lahadi ta nuna cewa wannan ƙaruwa ta samo asali ne sakamakon daidaituwar ayyukan haƙo mai da kuma inganta tsarin bututun mai.


A cewar rahoton, Nijeriya ta samar da gangar ɗanyen mai miliyan 1.56 a kowace rana a watan Yuni, adadin da ya haura gangar mai miliyan 1.5 a rana da OPEC ta amince ƙasar ta riƙa samarwa.


Baya ga haka, alƙaluma sun nuna cewa Nijeriya ta kai kashi 104 cikin 100 na bin ƙa’idodin ƙungiyar OPEC kan yawan man da ake haƙowa.


Idan aka haɗa da nau’in mai na condensates, wanda ba ya ƙarƙashin tsarin rabon OPEC, jimillar man da Nijeriya ta samar ta kai kimanin gangar mai miliyan 1.735 a kowace rana a watan Yuni, idan aka kwatanta da gangar mai miliyan 1.700 a rana da aka samar a watan Mayu.


Reuters ya ƙara da cewa wannan shi ne wata na huɗu a jere da ake samun ƙaruwa a yawan ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa.


Har ila yau, adadin da aka samar a watan Yuni shi ne mafi girma da ƙasar ta samu tun watan Afrilun shekarar 2020, wanda hakan ya sa ya zama mafi girma cikin watanni 74.


Masana sun danganta wannan ci gaba da daidaituwar ayyukan haƙar mai, tare da rashin matsalolin toshe manyan bututun mai, lamarin da ya taimaka wajen ƙara yawan haƙo da kuma fitar da ɗanyen mai zuwa kasuwannin duniya.