Gwamnatin Birtaniya ta sanar da sanya Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) cikin jerin ƙungiyoyin da aka haramta tare da ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
Matakin, wanda aka shafe shekaru ana muhawara a kansa a Birtaniya, ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu 'yan majalisa da 'yan siyasa suka dade suna yi na ɗaukar irin wannan hukunci.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan wasu hare-hare da aka kai kan Yahudawan Birtaniya, tare da amincewar majalisar ƙasar da sabuwar dokar tsaron ƙasa da Firaminista Keir Starmer ya yi alƙawarin aiwatarwa.
A baya, dokokin Birtaniya na haramta ƙungiyoyin ta'addanci ba su kan shafi ƙungiyoyin da gwamnatoci ke marawa baya.
Sabuwar dokar ta haramta ba da duk wani tallafi ga rundunar ta IRGC, ko kuma yin kalamai da ke nuna goyon baya ga manufofi da aƙidarta.