A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Hadin Kai, mai yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin ƙasar ta fitar, ta ce an gano mutanen ne bayan da sojoji suka ƙwato wata kyamara a yayin wani artabu da mayaƙan ISWAP a yankin Cross Kauwa da ke Jihar Borno.

Sanarwar ta ce hotuna da bayanan da ke cikin kyamarar sun taimaka wajen gano mutanen uku. Daga cikinsu akwai wani Bafalasɗine mai suna Abu Ishaq, wanda rundunar ta ce shi ne babban mai horas da mayaƙan ƙungiyar.

Haka kuma, an gano wani mai suna Abu Thaiba, wanda aka bayyana a matsayin likitan ISWAP. Sai kuma wani mutum na uku, wanda har yanzu rundunar ke ci gaba da bincike domin gano ƙasarsa, sunansa da kuma irin rawar da yake takawa a cikin ƙungiyar.

Rundunar ta ce an ƙwato kyamarar ne bayan wani mai ɗaukar hotunan ƙungiyar ya yar da ita yayin da ake fafatawa da sojoji. A cewarta, kyamarar na ɗauke da hotuna da wasu muhimman bayanai da ke nuna yadda mayaƙan ISWAP ke shirya hare-hare kan sansanonin sojoji.

An daɗe ana zargin cewa wasu 'yan ƙasashen waje na taka rawa a ayyukan ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram, kuma rundunar ta ce wannan sabon bincike zai taimaka wajen ƙara fahimtar hanyoyin da ƙungiyar ke gudanar da ayyukanta.