Wani sabon bincike ya nuna cewa sama da mutum 2,700 sun rasa rayukansu sakamakon tsananin zafin rana da aka fuskanta a Ingila da Wales tsakanin watan Mayu da Yuni na wannan shekara.

Masu bincike daga Jami'ar Imperial College London, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Yanayi ta Birtaniya da kuma Makarantar Kula da Lafiyar Al'umma ta London, sun bayyana cewa sauyin yanayi ya taka muhimmiyar rawa wajen tsananta zafin da ya haifar da waɗannan mace-mace.

A cewar rahoton, mafi yawan mace-macen sun faru ne a lokacin da aka samu mummunar guguwar zafi a watan Yuni, lokacin da yanayin zafi ya kai digiri 37.7 a ma'aunin Celsius a wasu sassan ƙasar.

Masu binciken sun ce wannan al'amari ya ƙara nuna irin babbar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar al'umma, tare da jaddada buƙatar ɗaukar matakan kare rayukan jama'a daga tasirin matsanancin zafi.