Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun sakandire, domin ba da damar sake nazarin matakin tare da ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan shawarwari da ra'ayoyi da aka samu daga jama'a kan shirin.
Tun da farko, ma'aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin rajistar jarrabawar daga naira 27,000 zuwa naira 50,000, wanda aka shirya fara aiwatarwa daga shekarar 2027.
Ma'aikatar ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalolin tattalin arziki sun sa kuɗin da ake karɓa a halin yanzu ba ya wadatar wajen gudanar da jarrabawar yadda ya kamata.
Sai dai sanarwar ta jawo ce-ce-ku-ce da suka daga sassa daban-daban na al'umma. Mutane da dama sun nuna damuwa cewa ƙarin kuɗin zai ƙara wa iyaye da masu kula da ɗalibai nauyin kuɗi, tare da yiwuwar janyo wasu ɗalibai su kasa ci gaba da karatu.
Hakan ya sa aka riƙa yin kira ga gwamnati da ta sake duba matakin, kafin daga bisani ta sanar da dakatar da shirin.
Ma'aikatar Ilimi ta ce tana godiya da shawarwari da gudunmawar da 'yan Najeriya suka bayar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da yin nazari kan batun kafin ɗaukar mataki na gaba.