Tsohon babban kwamandan rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM), Janar Frank McKenzie mai ritaya, ya ce sojojin Amurka na da ƙarfin da za su iya ƙwace iko da mashigar Hormuz idan shugaban ƙasar ya ba da umarnin yin hakan.
A wata hira da kafar yaɗa labarai ta CBS, Janar McKenzie ya bayyana cewa irin wannan mataki zai buƙaci tura manyan jiragen ruwan yaƙin Amurka zuwa yankin. Ya ce, duk da cewa rundunar sojin ruwan Amurka ba ta nuna aniyar aiwatar da hakan a yanzu ba, tana da cikakken ƙarfin yin hakan idan bukatar ta taso.
Kalaman tsohon kwamandan sun zo ne a matsayin martani ga iƙirarin da Iran ta yi na cewa ta rufe mashigar Hormuz tare da kai hare-hare kan wasu jiragen ruwan kasuwanci da ke zirga-zirga a yankin.
McKenzie ya kuma ba da shawarar cewa Amurka ta yi la'akari da ƙwace iko da tsibirin Kharg, yana mai cewa hakan na iya zama wata hanya ta matsa wa Iran lamba domin ta sake buɗe mashigar Hormuz da kuma komawa teburin tattaunawa.