Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gana da Mataimakin Sakataren Amurka, Frank Garcia, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Taron ya mayar da hankali ne kan bunƙasa haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci, inganta musayar bayanan sirri, da kuma ƙarfafa dabarun da ƙasashen biyu ke amfani da su wajen fuskantar barazanar tsaro.
Bangarorin biyu sun kuma yi nazari kan irin ci gaban da aka samu a haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya da yankin Afirka ta Yamma.
Ganawar na daga cikin ƙoƙarin da Najeriya da Amurka ke yi na zurfafa alaƙar tsaro da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen daƙile ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da ke addabar yankin.