Gwamnatin kano ta jaddada kudurin hukumar KHETFUN na inganta asibitocin jihar cike da gaskiya da rikon amana wajen kashe kudin hukumar.
Babbar Sakatariyar hukumar ta Kano State Health Trust Fund (KHETFUND), Dakta Fatima Usman Zahraddeen ce bayyana hakan, yayin wata ziyarar tantance ayyukan da aka aiwatar bayan bayar da tallafi a Babban Asibitin Gwarzo, inda aka duba yadda aka aiwatar da ayyukan da darajarsu ta kai Naira miliyan 42,397,000.
A yayin ziyarar, Babbar Sakatariyar hukumar, wadda Daraktan Ayyuka na Dakta Lawan Adamu ya wakilta, ta tabbatar da cewa an kammala ayyukan da suka haɗa da samar da wutar lantarki ta hasken rana (Solar) da kuma sayo muhimman kayan aikin likitanci.
Hukumar KHETFUND ta fitar da kuɗaɗen aikine ne a ranar 2 ga Disamba, 2025.
Da take magana yayin gudanar da ziyarar gani da Ido, Dakta Fatima Usman Zahraddeen ta bayyana cewa wannan ziyarar tantancewa na daga cikin tsarin sa ido da kimanta ayyukan KHETFUND, wanda aka tsara domin tabbatar da cewa duk wani aikin da Asusun ya ɗauki nauyi an aiwatar da shi yadda ya kamata kuma yana amfanar marasa lafiya da ma'aikatan lafiya.