Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Sanarwar ta ce jirgin Air Peace ne zai gudanar da jigilar, inda zai tashi daga Afirka ta Kudu da ƙarfe 1:30 na safe, inda ake sa ran zai sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Mohammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:30 na safe.

Tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da jirage huɗu na aikin kwaso 'yan Najeriya zuwa gida, inda ta dawo da ɗaruruwan mutane sakamakon hare-haren ƙiyayya ga baƙi (xenophobia) da kuma matsalolin tsaro da suka faru a wasu sassan Afirka ta Kudu.

Shirin kwaso mutanen ya shafi 'yan Najeriya ne da suka nuna sha’awarsu ta komawa gida saboda waɗannan hare-hare.

A rukunin da ya gabata, an dawo da mutane 40 zuwa Najeriya.

Ma'aikatar Harkokin Waje ta sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da muradun 'yan Najeriya a duk inda suke a duniya, tare da gode wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka ba da gudummawa wajen gudanar da wannan shirin na kwaso 'yan ƙasa gida.