Matatar Man Dangote ta fara amfani da farashin dala wajen sayar da man fetur da sauran kayayyakin da take samarwa, maimakon tsarin farashin naira da aka saba amfani da shi.


Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan yadda Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ke sayar wa matatar mafi yawan ɗanyen man da take buƙata a farashin dala.


A cewar rahotannin, sauyin tsarin farashin na nufin cewa masu sayen man fetur daga matatar za su biya bisa farashin dala, lamarin da masana ke ganin zai iya sauya yadda ake ƙayyade farashin man fetur a kasuwar cikin gida.


Masana tattalin arziki sun bayyana cewa sabon tsarin na iya ƙara matsin lamba kan farashin man fetur idan darajar dala ta ci gaba da ƙaruwa a kan naira. Sun kuma yi gargadin cewa hakan na iya ƙara tsadar rayuwa tare da ƙara wa masu ƙaramin ƙarfi wahala.


Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken tasirin da sabon tsarin zai yi kan farashin man fetur a gidajen mai ba, yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da nazarin matakin.