An ƙaddamar da wannan tsari ne ta hannun Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja, da nufin daidaita shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu da kuma magance abin da hukumomi suka bayyana a matsayin tatsar iyaye kudi da tsada da nuna isa a makarantu masu zaman kansu.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Ayyukan Yaɗa Labarai na Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta jihar, Yunusa Ibrahim, ya fitar, gwamnatin ta ce maimakon bukukuwan kammala karatu, makarantu su riƙa gudanar da Bukukuwan Jawabi da Raba Kyaututtuka domin karrama ɗalibai da suka yi fice a karatu, kyawawan ɗabi'u, ƙwarewar shugabanci da sauran manyan nasarori.

Sanarwar ta bayyana cewa yawaitar shirya bukukuwan kammala karatu cikin almubazzaranci da ɗora wa iyaye nauyin kuɗaɗe da bai dace ba, tare da haifar da gasa mara amfani tsakanin makarantu.

Gwamnatin ta ƙara da cewa da dama daga cikin waɗannan bukukuwa sun kauce daga ainihin manufarsu ta ilimi, inda kashe kuɗaɗe masu yawa da kuma neman riba suka mamaye abin da ya kamata ya kasance bikin yabawa nasarorin ilimi.

Ta ce sabon umarnin na da nufin dawo da daidaito, ƙarfafa tarbiyya da kuma tabbatar da cewa shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu sun  mayar da hankali kan sakamakon ilimi da ƙwazon ɗalibai.

Domin tabbatar da bin wannan umarni, Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da sauran masu ruwa da tsaki za su fara gangamin wayar da kai a faɗin jihar domin ilmantar da makarantu da al'umma game da sabon tsarin.

Haka kuma, an ɗora wa jami'an yaɗa labarai da masu wayar da kan al'umma alhakin tattaunawa da shugabannin makarantu, iyaye da al'ummomi domin su fahimci sabon umarnin tare da tabbatar da aiwatar da shi yadda ya kamata.