Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad a ranar Talata ya ƙaryata wani rahoto na The New York Times da ke zargin cewa hukumar leken asiri ta Isra'ila, Mossad, ta nemi ɗaukar shi aiki haka kuma an yi masa ɗaurin-talala, inda ya bayyana ikirarin a matsayin “ƙarya tsagwaronta.”

A cikin wata sanarwa, ofishin Ahmadinejad ya zargi jaridar da wallafa rahotannin da aka ƙiƙira don yaudarar ra'ayin jama'a da ƙara haddasa rarrabuwar kai a cikin gida a Iran.

Ofishin ya kuma ƙaryata cewa Ahmadinejad yana ƙarƙashin ɗaurin-talala, inda ya ce wannan ikirarin an ƙirƙire shi ne domin tallafa wa abin da suka kwatanta a matsayin ikirarin jaridar “marar ma'ana”.

“Muna musanta gaba ɗaya dukkan waɗannan ƙarairayin da The New York Times ta yayata,” in ji sanarwar.

The New York Times ruwaito a ranar Litinin ta ruwaito cewa Mossad ta yi ƙoƙari a shekarun baya don ta rinjayi Ahmadinejad ya haɗa kai da Isra'ila kuma sun ɗauke shi a matsayin mai yiwuwar wanda zai jagoranci Iran.

Rahoton ya zargi cewa wannan shirin wani ɓangare ne na babban yunkurin Isra'ila na kawo sauyin wamnati a Iran bayan hare-haren farko da aka kai kan manyan shugabannin Iran.