Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano yadda abin ya faru da kuma tabbatar da gaskiya.
Makinde ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X, inda ya jaddada muhimmancin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Ya ce ya kamata a bayyana sakamakon binciken ga jama’a domin tabbatar da gaskiya, tare da ba al’umma cikakken bayani da zai kawar da ruɗani da cece-kuce da har yanzu ke ci gaba da gudana kan lamarin.
Gwamnan ya ƙara da cewa bayyana gaskiyar abin da ya faru zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da kuma tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace bisa sakamakon binciken.