Majalisar Wakilan Nijeriya ta janye kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar kan kafa ‘yan sandan jihohi, inda ta ci gaba da duba sabon kudirin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike mata kan batun.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Majalisar ta bayyana hakan ne a zaman da ta gudanar ranar Talata, inda ta yi karatu na farko da na biyu ga kudirin da bangaren zartarwa ya gabatar.
Bayan kammala karatun kudirin, Majalisar ta tura shi zuwa kwamitinta kan gyaran kundin tsarin mulki domin ci gaba da nazari da tantance muhimman tanade-tanadensa.
Matakin na nufin dakatar da ci gaba da aikin kan kudirin da majalisar ta gabatar da kanta, yayin da ta mayar da hankali kan sabon kudirin da Gwamnatin Tinubu ta gabatar.
Ana sa ran kwamitin zai yi cikakken nazari kan kudirin kafin ya dawo zauren Majalisar domin ci gaba da tattaunawa da kuma yanke hukunci a kansa.