Ga muhimman abubuwan da ya kamata ka sani kafin fafatarwar Faransa da Sifaniya a wasan kusa da na karshe na Kofin Duniya na 2026:
Wannan wasa zai tantance wacce kasa za ta kai wasan karshe na gasar, yayin da wacce ta sha kashi za ta buga wasan neman matsayi na uku.
Kasar Faransa da safaniya sun buga wasanni 38 inda kasar safaniya tayi nasara sau 18 kazalika faransa tayi nasara a wasanni 13, inda sukayi wasanni canjaras sau 7.
Wasan zai gudana a Dallas Stadium da ke Arlington, Texas, inda za'a fara wasa da misalin 8:00 na dare agogon Najeriya.