Kotun Koli ta India ta yi watsi da wata ƙara da wani mazaunin birnin Mumbai ya shigar, wadda ke ƙalubalantar amincewar da aka bai wa fitaccen jarumin Bollywood Shah Rukh Khan da matarsa Gauri Khan na gyara da faɗaɗa gidansu mai suna Mannat da ke yankin Bandra.
Kotun ta bayyana cewa masu gidaje na da 'yancin gyarawa ko faɗaɗa gidajensu muddin suna bin dokokin ƙasa da ƙa'idojin da suka dace.
Mai ƙarar ya yi zargin cewa ba a bi dukkan ƙa'idojin doka da na muhalli ba wajen amincewa da aikin. Lauyansa ya kuma yi iƙirarin cewa ya kamata a samu sahalewar Ma'aikatar Muhalli, Gandun Daji da Sauyin Yanayi ta India, musamman idan kuɗin aikin ya zarce rupee miliyan 50 (Rs 5 crore).
Sai dai yayin sauraron shari'ar, alkalan Kotun Koli sun nuna shakku kan dalilin shigar da ƙarar. Babban Alƙali Surya Kant ya ce gidan mallakar mutum ne, kuma masu gidan na da damar yin gyare-gyare muddin suna mutunta dokokin ƙasa.
Lauyan mai ƙarar ya roƙi kotun da ta mayar da batun zuwa Kotun Kula da Muhalli ta Ƙasa (NGT) domin sake dubawa, amma Kotun Koli ta ƙi amincewa da buƙatar.
Kotun ta kuma jaddada cewa shaharar Shah Rukh Khan ba ta da wani tasiri a kan yadda aka gudanar da shari'ar.