Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Wakilai ta yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 kwaskwarima domin samar da damar kafa rundunar 'yan sandan jihohi (State Police), yana mai bayyana cewa mataki nada da matuƙar muhimmanci wajen sake fasalin tsaron kasarnan domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, shugaban ƙasar ya miƙa Kudirin gyaran kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (Kafa Rundunar 'Yan Sandan Jihohi), 2026, domin majalisar ta yi nazari tare da duba yiwuwar amincewa da shi.
Tinubu ya bayyana cewa kudirin gyaran kundin tsarin mulkin na da nufin samar da ingantacciyar hanyar doka da za ta ba jihohi damar kafa rundunonin 'yan sandansu, yana mai cewa an gina kudirin ne bisa aikin da Majalisar Wakilai ta riga ta fara gudanarwa kan wannan batu.
A cewarsa, kudirin ya kuma ƙunshi wasu ƙarin tanade-tanade da za su tabbatar da cewa tsarin rundunonin 'yan sanda biyu — na tarayya da na jihohi — zai samu aiwatarwa cikin sauri da inganci domin amfanin 'yan Najeriya.
Ya ce, "Wannan kudiri wani muhimmin ɓangare ne na dabarun gwamnatina na sake fasalin tsarin tsaron Najeriya domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar ƙasa yadda ya kamata."
Shugaban ƙasar ya bayyana kwarin gwiwar cewa Majalisar Wakilai za ta gaggauta nazari tare da amincewa da kudirin.
Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan wasu rahotanni dake cewa majalisar wakilai ta jingine kudirin samar da yan sanda jihohin
gudanar da rundunonin 'yan sandansu a hukumance, tare da ci gaba da aiki kafada da kafada da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya.