Hukumar Kula da Tsaron Jiragen Sama ta Tarayyar Turai ta fitar da gargaɗi ga kamfanonin jiragen sama kan amfani da sararin samaniyar Bahrain, Kuwait, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma yankunan da ke saman Tekun Oman.
Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙaruwar rashin tabbas na tsaro a yankin, wanda ya samo asali daga ci gaba da ayyukan soji da kuma yiwuwar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa (drones).
A cikin sanarwar, hukumar ta ce akwai yiwuwar jiragen sama su fuskanci barazana idan suka ratsa ta wannan yanki, don haka ta buƙaci kamfanonin jiragen sama su yi taka-tsantsan tare da bin dukkan shawarwarin tsaro.
Hukumar ta ce wannan gargaɗi zai ci gaba da aiki har zuwa 29 ga Yulin, tare da ƙara da cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda al'amuran tsaro ke gudana domin ɗaukar matakan da suka dace idan buƙatar hakan ta taso.
Gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin, inda ake musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka, yayin da wasu ƙasashen yankin ke karɓar sansanonin sojin Amurka da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan soji.