Shekara guda bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, abokansa da na hannun damansa sun gudanar da taron tunawa da shi a Abuja, inda suka yi waiwaye kan rayuwarsa da irin gudunmawar da ya bayar ga siyasar Najeriya.
Marigayi Buhari na daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya da suka yi fice wajen samun gagarumar goyon bayan jama'a. Tun daga lokacin da yake neman shugabancin ƙasa har zuwa nasarar da ya samu a zaɓen shekarar 2015, ya kasance yana samun ɗimbin ƙuri'u daga magoya bayansa.
Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga Yulin 2025 a wani asibiti da ke Landan, shekaru biyu bayan kammala wa'adinsa na shugabancin ƙasa.
Bayan rasuwarsa, an fara tambayar ko akwai wani da zai iya gaje shi wajen haɗa kan magoya bayansa da kuma ci gaba da tafiyar da aƙidar siyasarsa.
Masana harkokin siyasa sun ce tun kafin rasuwarsa an fara samun rarrabuwar kawuna tsakanin wasu daga cikin manyan makusantansa. Wasu sun ci gaba da mara wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yayin da wasu suka ɗauki matsayar adawa da gwamnatin tare da bayyana rashin gamsuwarsu da wasu manufofinta.
Duk da wannan rarrabuwar kai, Buhari bai taɓa fitowa fili ya nuna goyon baya ga wani ɓangare ba kafin rasuwarsa.
Masanin harkokin siyasa, Kabir Sufi, ya bayyana cewa rarrabuwar kawunan da ake gani tsakanin makusantan Buhari ta samo asali ne tun kafin ƙarshen mulkinsa, kuma ta ƙara bayyana bayan rasuwarsa, yayin da kowane ɓangare ke ƙoƙarin sake tsara matsayinsa a siyasar Najeriya.