Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kamo Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙirar wata hukumar bogi tare da ikirarin cewa shi ne Darakta Janar na hukumar PFIPC.
Kotun ta bayar da umarnin ne bayan Adeyemi ya gaza halartar zaman da aka shirya domin fara shari’ar da ake yi masa kan zarge-zargen da ake fuskanta.
Rahotanni sun ce hukuncin kotun na nufin jami’an tsaro su kamo wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar.
Har yanzu dai ba a samu wata sanarwa daga Adeniyi Adeyemi ko lauyansa ba kan rashin halartar zaman kotun.