Bayan da jam'iyyar APC ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a matsayin 'yan takararta na shugaban ƙasa da mataimakinsa a zaɓen 2027, masana harkokin siyasa sun yi nazari kan tasirin ci gaba da amfani da tikitin Muslim-Muslim.

Matakin ya kawo ƙarshen jita-jitar da ta yi ta yawo cewa mai yiwuwa Shugaba Tinubu ya sauya mataimakinsa saboda matsin lamba daga wasu ƙungiyoyi da suka yi kira da a samar da daidaito tsakanin addinai a tikitin shugaban ƙasa.

Masana sun bayyana cewa batutuwan addini da yanki na ci gaba da kasancewa muhimman abubuwa a siyasar Najeriya, musamman wajen zaɓen shugaban ƙasa.

Masanin kimiyyar siyasa, Dakta Kabiru Sufi, ya ce babban dalilin ci gaba da tikitin Muslim-Muslim shi ne lissafin siyasa da kuma ƙoƙarin tabbatar da samun goyon baya daga yankunan da jam'iyyar ke ganin suna da muhimmanci wajen cin zaɓe.

A cewarsa, idan tikitin ya sake samun nasara a zaɓen 2027, hakan na iya rage tasirin batun daidaita addini wajen zaɓen 'yan takara, tare da bai wa jam'iyyu damar mayar da hankali kan wasu dalilai kamar ƙwarewa da dabarun siyasa.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa ko da tikitin ya yi nasara, batun ba zai rasa masu adawa ba, musamman a yankunan da batun addini ke da tasiri a siyasa.

Shi ma Farfesa Yahaya Tanko na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce tikitin Muslim-Muslim ya jawo muhawara mai zafi tun a zaɓen 2023, kuma akwai yiwuwar irin wannan muhawarar ta sake maimaituwa a zaɓen 2027.

A cewarsa, yadda aka kaɗa ƙuri'u a zaɓen 2023 ya nuna cewa batun addini ya yi tasiri a zaɓin wasu masu kaɗa ƙuri'a, lamarin da ya nuna cewa batun na ci gaba da kasancewa mai muhimmanci a siyasar ƙasar.

Wasu daga cikin lokutan da aka yi tikitin Muslim-Muslim a Najeriya

  • 1993: MKO Abiola da Babagana Kingibe (SDP) sun yi takara tare a matsayin shugaban ƙasa da mataimakinsa.
  • 2019: Nasir El-Rufai da Hadiza Sabuwa Balarabe sun yi takarar gwamna da mataimaki a Kaduna.
  • 2023: Uba Sani da Hadiza Sabuwa Balarabe sun yi takarar gwamnan Kaduna da mataimakiyarsa.
  • 2023: Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima sun yi takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Masana sun ce tasirin tikitin Muslim-Muslim a zaɓen 2027 zai bayyana ne bayan sakamakon zaɓen, wanda zai nuna ko wannan tsari zai ci gaba da zama abin karɓuwa a siyasar Najeriya ko kuwa zai ci gaba da haifar da muhawara tsakanin al'umma.