Ƙungiyar Manchester United ta tabbatar da ɗaukar mai tsaron raga na ƙasar Wales, Karl Darlow, bayan ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu, tare da zaɓin ƙara masa wata shekara idan ya cika sharuɗɗan da ƙungiyar ta gindaya.

Darlow ya koma Old Trafford ne bayan ƙarewar kwantiraginsa da Leeds United a ƙarshen kakar wasan da ta gabata. Duk da cewa Leeds ta ba shi sabon tayin kwantiragi, golan mai shekaru 35 ya zaɓi komawa Manchester United.

Rahotanni sun ce zuwan Darlow na iya ƙara ƙarfafa hasashen cewa golan Turkiyya, Altay Bayındır, na dab da barin Manchester United, bayan an daɗe ana alakanta shi da komawa ƙungiyar Beşiktaş.

Darlow ya kammala kakar wasan da ta gabata a matsayin golan farko na Leeds United a ƙarƙashin koci Daniel Farke, inda ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin ƙungiyar.

A tsawon aikinsa, ya buga wasanni 279 a matakin ƙungiyoyi, sannan ya wakilci ƙasar Wales sau 15.

Ana sa ran Darlow zai fara kakar wasa a matsayin mataimakin sabon golan farko na Manchester United, Senne Lammens. Saboda Lammens zai kasance hutu bayan wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da Belgium ta buga, ana sa ran Darlow zai samu damar taka rawa a wasannin shirin tunkarar sabuwar kakar wasa (pre-season), wanda zai fara da wasan sada zumunta da Wrexham a birnin Helsinki ranar 18 ga Yuli.