Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da shirin yafewa, karɓar makamai da kuma sake shigar da tubabbun 'yan ta'adda cikin al'umma, duk da ci gaba da suka da kiraye-kirayen da ake yi na dakatar da shirin.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta bayyana cewa ta fitar da wani kundin tsare-tsare da zai jagoranci yadda za a aiwatar da shirin, domin tabbatar da karɓar makamai daga hannun tubabbun 'yan ta'adda, rusa ƙungiyoyinsu da kuma mayar da su cikin al'umma ta hanyar da ta dace.

Matakin na zuwa ne yayin da wasu 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna rashin amincewarsu da shirin, suna masu kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen bai wa tubabbun 'yan ta'adda afuwa, tare da fifita hukunta waɗanda suka aikata manyan laifuka.

Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa shirin na daga cikin dabarunta na haɗa matakan soja da na sasanci domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, tana mai jaddada cewa ba za ta janye daga aiwatar da wannan tsari ba duk da ce-ce-ku-cen da ya haifar.