Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta karɓi jerin sunayen 'yan takarar jam'iyyar ADC da ɓangaren da Sanata David Mark ke jagoranta ya gabatar domin zaɓen shekarar 2027.

Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, ya ce an bai wa ɓangaren David Mark damar amfani da tsarin lantarki na hukumar wajen gabatar da sunayen 'yan takara, bisa hukuncin kotu da ya tabbatar da matsayin shugabancinsa.

A cewarsa, ɓangaren ya gabatar da sunayen 'yan takara 471, waɗanda suka haɗa da:

  • 'Yan takarar shugaban ƙasa biyu,
  • 'Yan takarar majalisar dattawa 109,
  • Da kuma 'yan takarar majalisar wakilai 360.

Sai dai ya bayyana cewa INEC ba ta karɓi wani jerin sunaye daga ɓangaren Nafiu Bala Gombe ba, yana mai cewa babu wata doka ko hukuncin kotu da ya ba wannan ɓangare damar gabatar da sunayen 'yan takara.

A martaninta, jam'iyyar ADC ta yi maraba da bayanin INEC, tare da zargin Nafiu Bala da yaudarar jama'a ta hanyar ikirarin cewa ya samu damar amfani da tsarin hukumar wajen gabatar da 'yan takara. Jam'iyyar ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan lamarin tare da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu da hannu.

Sai dai INEC ta bayyana cewa har yanzu tana jiran cikakken kwafin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rikicin shugabancin jam'iyyar kafin ta fitar da matsayinta na ƙarshe.

A baya, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya hana INEC amincewa da tarukan zaɓen shugabannin jihohi da kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark ya gudanar. Duk da haka, jam'iyyar ADC ta ce wannan hukuncin ya shafi tarukan jam'iyya ne kawai, ba ya shafar sahihancin zaɓen fidda gwani ko jerin sunayen 'yan takarar da aka gabatar domin zaɓen 2027.