Fitaccen mawallafin bidiyon barkwanci da masu sukar al'amuran siyasa, Bello Galadanci, wanda aka fi sani da Dan-Bello, tare da matarsa Sahura, sun buɗe sabon gidan cin abinci a birnin Guangzhou da ke ƙasar China.

Guangzhou, wanda ake kira Canton, na daga cikin manyan biranen lardin Guangdong a kudancin China. Birnin ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci, masana'antu da sufuri, kuma yana kusa da Hong Kong da Macau.

'Yar kasuwar sayar da tufafin mata, Farida Musa Kalla (FMK), ta kai ziyara gidan cin abincin, inda ta yaba da ingancin abincin da ake samarwa.

A cewarta, wannan ne karo na farko da ta haɗu da Dan-Bello da matarsa Sahura ido-da-ido, kuma ta bayyana cewa abincin da suke girkawa yana da inganci sosai.

Kafin buɗe wannan gidan cin abinci, an fi sanin Dan-Bello a matsayin malamin makarantar firamare a China, tare da gudanar da kasuwanci ta kafafen sada zumunta ta hanyar shafinsa da aka fi sani da "Kasuwar Bello."

Buɗe gidan cin abincin na nuni da wani sabon mataki na faɗaɗa harkokin kasuwancinsa a ƙasar China.