Dakarun (IRGC) sun bayyana cewa mashigar ruwan Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Amurka ta dakatar da hare-haren da take kai wa ƙasar.
Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da sojojin Amurka suka sake kai hare-hare kan wasu wuraren da suka haɗa da tashoshin jiragen ruwa a Iran.
IRGC ta kuma yi gargaɗin cewa za ta iya faɗaɗa hare-harenta zuwa wasu muhimman hanyoyin fitar da ɗanyen man fetur, lamarin da ka iya ƙara tayar da hankalin kasuwannin makamashi na duniya.
A daren da ya gabata, Iran da Amurka sun ci gaba da musayar hare-hare. Kafafen yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa an kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain, Kuwait da Jordan.
A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta ce ta shafe kusan sa'o'i bakwai tana kai hare-hare kan wasu wuraren da ta bayyana a matsayin muhimman cibiyoyin soji a Iran.
Yayin da ake nuna fargabar rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin barazanar ƙaddamar da sabbin hare-hare kan tashoshin samar da lantarki da manyan gadoji a Iran idan gwamnatin ƙasar ba ta koma teburin tattaunawa ba.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, ba a samu wata sanarwa mai zaman kanta da ta tabbatar da dukkan iƙirarin ɓangarorin biyu kan hare-haren da aka ruwaito ba.