Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa jajircewa da sadaukarwar da Sanata Oluremi Tinubu ta nuna a lokacin da take mamba a Majalisar Dattawa na daga cikin dalilan da Allah ya ɗaukaka ta zuwa matsayin Uwargidan Shugaban Ƙasa.
Barau ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin zaman Majalisar Dattawa, lokacin da yake goyon bayan wani kudiri da ke neman a fara ɗaukar halartar sanatoci a ƙarshen kowane zama, domin tantance waɗanda ke ci gaba da zama har zuwa lokacin da shugaban majalisa ya dage zaman.
A cewarsa, Oluremi Tinubu ta kasance tana zuwa majalisa da wuri, kuma ba ta barin zauren majalisa sai an kammala zaman, lamarin da ya nuna jajircewarta da himmarta wajen gudanar da ayyukan da aka zaɓe ta domin yi.
Sanata Barau ya ƙara da cewa sadaukarwa da ƙwazo wajen gudanar da aikin jama'a ba shugabannin majalisa kaɗai ke yaba wa ba, har ma Allah yana ba da ladarsa.
Ya ce irin wannan tsarin na ɗaukar halartar sanatoci a ƙarshen zaman zai ƙarfafa mambobin majalisar su kasance cikin zaman har zuwa ƙarshe, domin inganta gudanar da ayyukan majalisa.