Wasu da ake zargin 'yanbindiga ne sun kai hari makarantar sakandiren Gwamnati ta Opada-Olowa da ke ƙaramar hukumar Dekina a jihar Kogi, inda suka sace shugaban makarantar, jami'in sa ido na jarabawar NECO da kuma ɗalibai huɗu.


Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, yayin da ake gudanar da jarabawar NECO.


Shaidu sun bayyana cewa maharan sun shiga yankin suna harbe-harbe domin tarwatsa jama'a kafin su kutsa cikin makarantar. 


Bayan harin, an tarar da takardun jarabawa a warwatse a cikin azuzuwa da harabar makarantar, yayin da babu ɗalibai ko malamai a wurin.


An bayyana sunayen waɗanda aka sace da shugaban makarantar, Nyada Daniel, jami'in NECO, Solomon Audu, da ɗalibai huɗu.


Mazauna yankin sun ce adadin ɗaliban da aka sace bai yi yawa ba saboda a lokacin ɗaliban da ke rubuta darasin Turanci ne kaɗai suke jarabawa.


Rahotanni sun kuma ce maharan sun tuntubi iyalan wasu daga cikin waɗanda aka sace tare da neman kuɗin fansa domin a sake su.