Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kammala aikin kwaso 'yan ƙasar da suka maƙale a Afirka ta Kudu sakamakon ƙazancewar zanga-zangar ƙyamar baƙi da ta ɓarke a wasu sassan ƙasar.
A ranar Talata ne jirgi na ƙarshe kuma na shida, ɗauke da 'yan Najeriya 306, ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.
Hukumomi sun bayyana cewa, zuwa yanzu an kwaso fiye da 'yan Najeriya 1,200 a ƙarƙashin shirin gaggawa da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar domin dawo da 'yan ƙasar gida cikin aminci.
Ko da yake zanga-zangar ta kasance cikin lumana a wasu yankuna, ta rikide zuwa tashin hankali a wasu wurare, inda aka samu hare-hare, asarar rayuka da lalata dukiyoyi.
Gwamnatin Najeriya ta kuma bayyana aniyarta ta neman diya daga gwamnatin Afirka ta Kudu ga 'yan ƙasarta da suka yi asarar gidaje, sana'o'i da sauran kadarori sakamakon rikicin.
Hukumomin gwamnati sun ce za su ci gaba da tallafa wa waɗanda aka dawo da su tare da duba hanyoyin sauƙaƙa musu komawa rayuwa bayan dawowarsu Najeriya.