Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce Allah ne ya saka wa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, saboda jajircewa da ƙwazonta lokacin da take mamba a majalisar dattawa.


Barau ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar ranar Talata, bayan Sanata Abdul Ningi ya ba da shawarar a riƙa ɗaukar sunan sanatoci da su ka halarta a ƙarshen zaman domin karrama waɗanda ke zama har zuwa rufe zama.


A cewarsa, Oluremi Tinubu ce kan kasance ta farko wajen zuwa majalisar, kuma tana zama har zuwa ƙarshen zaman, yana mai cewa wannan jajircewa ce Allah ya saka mata da matsayin uwargidan shugaban kasa.


Ya ƙara da cewa ba shugabancin majalisa kaɗai ke karrama masu himma ba, har Allah ma yana saka wa waɗanda ke gudanar da ayyukansu da gaskiya da jajircewa, yana kira ga sanatoci da su ɗauki nauyin wakilcin al'umma da muhimmanci.