Yadda ake zargin hukumar VIO ta kano na tilastawa masu mota gwajin lafiyar mota da biyan kudi ta Opay din ma'aikaci Musa Abdullahi maimakon bankin hukumar.


Al'ummar Jihar Kano dake bin titin sharada hanyar UBA sun koka Kan yadda ma'aikatan hukumar kula da lafiyar ababan hawa VIO na Jihar kano ke tilasta musu biyan kudin duba lafiyar mota a asusun Opay na wani mai'aikacin kudi ( cashier) Mai dauke da sunan Musa Abdullahi a maimakon asusun Gwamnati


Masu korafin sun bayyana cewa a lokatu da dama jami'an hukumar Kan tsare tituna sun tatsar kudi a hannun direbobi musamman wadanda suka raina shigarsu ko suke ganin zasu kudi a gunsu.


Wakilinnmu Adamu Abdullahi daya ziyarci Ofishin hukumar dake wannan titi, ya rawaito cewa, ma'aikatan na tsayar da motocin ne tare da fara tambayarsu takardun moto zuwa lasisin tuki, daga nan ne kuma sai jami'an su nemi direban mota ya Shiga Ofishinsu da nufin za a duba masa Lafiyar motarsa cikin minti biyu, inda daga nan ne da mutum ya shiga sai a nemi ya biya kudi.


Wasu da Lamarin ya rutsa da su, Muhktar Muhammad mazaunin unguwar Indabawa, ya Shaidawa wakilinnmu cewa, an tsayar da shi tare da duba takardun motarsa, bayan an samu komai yadda doka ta tanada sai jami'in ya ce da shi ya Shiga a duba motar a kan Naira dubu uku kacal, da shigarsa kuma sai aka ce da Shi Naira dubu bakwai (7000) zai biya. Shima Mustafa Abdullahi ya shaida mana cewa baitaba Jin wannan dokar ba, kuma an Shiga hakkinsa domin akan hanyarsa ta neman abinci yake, haka kuma abunda yake Kan wasu Mata da aka tsayar da suka dauko yara daga makaranta.


Wani jami'i wanda daga dukan alamu shine ke jagorantar aikin kame da gami da tursasa biyan kudi a wannan ofishi na VIO dake sharada layin UBA, kamar Yadda masu korafin suka bayyana, ya sanarwa wakilinnmu cewa tun a Shekarar 2020 Gwamnati ta bijiro da wannan sabuwar doka, kuma sun yi ta Sanarwa a Gidajen radio tare da raba banoni dake Sanar da al'umma dokar. batun da Sama da mutum Goma da wakilinmu ya tarar a ofishin ya kuma ji ta bakinsu suka musanta.


Kuma babban abun tashin hankali da fargabar da mutanen da sukayi zargin an tilasta musu biyan wannan kudi suka bayyana shine, yadda ake sanya kudin da aka tatsa a hannunsu a asusun Opay na jami'in hukumar mai suna Musa Abdullahi a maimakon asusun banki mai dauke da sunan hukumar, wanda hakan ya jefa shakku a zukatan masu korafin har suke zargin jami'an ne ke watadantar kudaden.


Kazalika kasa da mintuna goma da bullar jami'in namu wannan guri, jami'an hukumar dake aikin taro mutane akan titi suka yi batan dabo domin sanda jami'in namu yake barin yakin sharada titin UBA , babu su babu alamarsu.


Faruwar hakan ke da wuya Wakilin Ammascoradio Mustafa Bin Adam ya tuntubi kakakin hukumar VIO na Jihar kano don Jin tabakinsa Kan Ko suna da masaniya ya ce zai nemu, awanni uku zuwa hudu muka ji Kira da sunan controller ne na hukumar Yana cewa mudan dakata fitar da labarin sunan suna zaman gaggauwa PRO zai nemi.


Sai dai har zuwa asbahin wannan rana ta Alhamis babu Kiran wayar PRO ko sakon waya Kan wannan batu.


Akwai dai bukatar Gwamnati a Jihar kamar kano ta rika sanya idanu Kan irin wadannan hukumomi da ake zargi da tatsar mutane kudi suna sanyawa a aljihu musamman idan akai la'akari da halin matsin rayuwa da mutane ke ciki.


Idan Allah yasa Hukumar VIO ta jihar kano ta magantu zaku ji