Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori kusan 48 da ake alaƙanta su da tsohon Ministan Shari'a kuma tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami.
Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayan ta amince da buƙatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar. Kotun ta ce waɗanda suka yi iƙirarin mallakar kadarorin sun kasa gabatar da gamsassun hujjojin da ke nuna cewa sun mallake su ne ta hanyar halastacciya.

Mai shari'ar ta bayyana cewa shari'ar ba ta shafi tantance wanda ya mallaki kadarorin ba ne, sai dai tana duba ko kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin sun fito ne daga hanyoyin da doka ta amince da su.
Daga cikin kadarorin da kotun ta ba da umarnin a ƙwace akwai Gidan Rediyon Rayhan, Jami'ar Rayhan, wasu otal-otal, kamfanoni da kuma rukunin gidaje na alfarma.

Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da buƙatun da Abubakar Malami, wasu daga cikin 'yan uwansa da kuma wasu kamfanoni masu alaƙa da kadarorin suka gabatar na neman a soke umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi da aka bayar tun da farko.
Sai dai kotun ba ta amince da ƙwace dukkan kadarorin da EFCC ta nema ba. Hukumar ta nemi a ƙwace kadarori 57, amma kotun ta amince da ƙwace kusan 48 daga cikinsu.

Mai shari'ar ta dogara da tanadin Sashe na 17 na Dokar Almundahana da Sauran Laifuka wajen yanke hukuncin.
Sai dai kotun ta jaddada cewa umarnin ƙwace kadarorin ba yana nufin an same Abubakar Malami ko wani daga cikin iyalansa da laifin aikata wani laifi ba, domin shari'ar ƙwace kadarori ta bambanta da shari'ar gurfanar da mutum kan aikata laifi.